Babban Limamin masallacin Juma’a na Usman Bn Affan a Kofar Gadon Kaya cikin karamar hukumar Gwale Dr. Aliyu Yunus, ya bayyana cewa soyayyar Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba abu ne da ake iya nunawa da baki kaɗai ba, sai dai tana bukatar a tabbatar da ita ta hanyar bin koyarwarsa da aikata abin da ya yi umarni da shi.
Dr. Yunus ya yi wannan bayani ne yayin gabatar da hudubarsa ta sallar Juma’a , inda ya ce, “Masoyin Annabi na gaskiya shi ne wanda yake bin tafarkinsa a zahiri ba a boye ba, sannan yana aikata sunnarsa, yana kaucewa bidi’a, kuma yana da halaye irin na Annabi kamar aikata gaskiya, adalci da jin ƙai.
Dr.Aliyu Yunus ya ce, ba duk wanda yake cewa yana son Annabi ba ne yake cikin masoyansa, domin soyayya ta gaskiya tana bayyana ne ta ayyuka da ɗabi’u masu kyau, ba ta maganganu ko waƙoƙin yabo kaɗai ba.
A cewarsa, Allah Madaukaki ya yi bayani a cikin Suratun Ali-Imran, aya ta 31, inda Ya ce:
Ka ce: Idan kuna son Allah, to ku bi ni, Allah zai so ku kuma Ya gafarta muku zunubanku. Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai.”
Dr. Yunus ya ce wannan aya ta tabbatar da cewa soyayyar Allah da ta Annabi ba ta tabbata sai da bin Annabi (S.A.W) a zahiri da aikace.
Ya ƙara da cewa, bin koyarwar Annabi shi ne hanyar samun rahamar Allah, da kuma alamar masoyi na gaskiya.
Saboda haka, ya yi kira ga Musulmai da su tabbatar da cewa soyayyarsu ga Annabi ta kasance ta gaskiya, ta hanyar bin sunnarsa, aikata alheri, da guje wa duk abin da zai sabawa koyarwarsa.
Ya kuma gargaɗi wadanda suke kiran kansu masoya Annabi amma suke fakewa da sukar wasu hadisansa ko koyarwarsa da ake kira wato (Yan Kala Kato)da su tuba su fadawa Magoya bayansu gaskiya.
A ƙarshe, malamin ya jaddada cewa, “Idan muka bi Annabi Muhammadu (S.A.W) da gaskiya, za mu more zaman lafiya, da haɗin kai da rahamar Ubangiji a cikin wannan duniya da lahira..

