Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, ICPC, ta bayyana cewa cire sunan kasar nan daga jerin kasashen da ake sa ido kan harkokin kudaden haramun (wanda ake kira FATF grey list) zai kara wa Najeriya da ‘yan kasarta daraja a idanun kasashen duniya.
Kwamishinan hukumar ICPC mai kula da jihohin Kano da Jigawa Ahamad Muhammad Wada a Jawabinsa na wayar da kan jama’a game da alfanun cire Najeriya daga rukunin kasashen duniya masu halarta kuɗaden haram yace matakin zai karfafa hadin kai tsakanin hukumomin tsaro,da bankuna, da cibiyoyin bincike kan kudi a Najeriya.
Ahamad Wada ya bayyana cewa cire Najeriya daga jerin ya zama wani muhimmin mataki da ke nuna amincewar duniya da tsarin da gwamnati ta gindaya domin tabbatar da gaskiya da tsabtace harkokin kudi.
Yace hakan Yana daga cikin kokarin Shugaban kasa Bola Tinubu wajen bada dama a yaƙi cin hanci da rashawa da tsananta bincike akan iyakokin Najeriya.
ICPC ta kara da cewa hakan zai saukaka mu’amalar ‘yan Najeriya da bankunan waje, tare da bude sabbin damar zuba jari da cinikayya tsakanin kasashen duniya.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa kasancewar Najeriya a jerin kasashen da ake sa ido ya jawo cikas ga harkokin kudi, musamman wajen samun bashi daga kasashen waje da kuma jinkirin mu’amalar kasuwanci.
Sun ce cire kasar nan daga jerin zai taimaka wajen farfado da amincewar duniya ga tattalin arzikin Najeriya da kuma kara jan hankalin masu zuba jari daga ketare.
Ahamad Muhammad Wada ya ce ICPC za ta ci gaba da aiki da sauran hukumomi kamar EFCC, CBN, da NFIU domin tabbatar da dorewar nasarar da aka samu.

