Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin sa ta koyi babban darasi daga yadda aka gano wasu daga cikin tallafin gwamnati ba ya kaiwa ga mutanen da aka tsara za’a baiwa daga wasu kananan hukumomin Kano musamman Shanono.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron sake baiwa Matan Kano tallafin kuɗi naira dubu 50 domin su ja jari.
Gwamna Yusuf yace matan Kano wadanda suka taka rawa wajen zaben gwamnatinsa a shekarar 2023 ba zasu zamo koma baya ba ,yana mai cewa sannu a hankali kowacce mace zata amfana da romon demokaradiyya.
TST Hausa ta rawaito cewa a mata 5,200 suka amfana da kuɗaden.
A wajen taron gwamnan ya rokesu da suyi amfani da kuɗaden ta hanyar da ta dace , musamman rungumar kananan sana’oi na dogaro da kai.
Saidai gwamnan ya nuna damuwa kan kura Kuran da aka samu a baya wajen gaza isar da tallafin da ake bayarwa ga matan ko kuma wadanda aka bayar dominsu.
Mun dauki darasi daga abin da ya faru a Shanono, inda aka gano cewa tallafin da aka tanada bai kai ga wadanda aka nufa da su ba. Wannan lamari ya zama izina gare mu wajen tabbatar da gaskiya da adalci a duk wani shiri na tallafi a nan gaba,” in ji Gwamnan.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati za ta dauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa tallafin gwamnati yana kaiwa kai tsaye ga marasa karfi, ba tare da karkatar da shi ko son rai ba.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da sanya ido kan yadda ake rabon tallafi domin tabbatar da gaskiya da rikon amana musamman ta hanyar amfani da sarakunan gargajiya da suka hada da hakimai da Dagatai da masu unguwa da Kuma Shugabanin kananan hukumomi.
Manufar gwamnatin mu ita ce taimakawa talakawa, da ba wai wasu su yi amfani da damar su karbe abin da ba nasu ba,” in ji shi.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da bullo da shirye-shiryen jin kai domin tallafawa marasa karfi a wannan lokaci da ake fama da kalubalen tattalin arziki a kasa.

