Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta tabbatar da janye auren da ake shirin daurawa tsakanin fitaccen jarumin TikTok da barkwanci mai suna Idris Mai Wushirya da Basira ‘Yar Guda, bayan samun rahotanni da ke nuna akwai sabani da rashin fahimta tsakanin ɓangarorin biyu.
A wani sakon murya da mataimakin babban kwamandan Hisba a bangaren ayyuka na musamman Dr Mujahedeen Aminuddeñ Abubakar ya aikewa TST Hausa yace bayan gwaje gwajen da sukayi saurayin da budurwarsa sai Hisba ta fahimci cewa sunyi hakan ne domin kwatar kansu daga hannun Kotu,a yanzu an janye Auren domin gudun rashin jituwa bayan auren nasu.
Yace hukumar ta ɗauki wannan mataki ne domin gujewa rikici da kuma tabbatar da cewa auren ya kasance cikin yardar juna da fahimtar duka masu ruwa da tsaki.
Rahotanni sun ce Hisba ta shiga lamarin ne bayan da aka samu ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta kan yadda aka tsara bikin, tare da zargin cewa wasu bayanai sun saba da ƙa’idojin aure na addinin Musulunci.
Dr Mujahedeen yace hukumar Hisbah zata mayar da mutanan biyu zuwa Kotu domin daukar mataki na gab.
TST Hausa ta rawaito cewa maganar auren Mai Wushirya ya janyo Cece-Kuce a shafukan sada zumunta na zamani,wanda har shi mai Wushiryar yayi wani bidiyo da yake cewa dama tsarota shi akayi ya amince da batun auren.

