Attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, wanda shi ne shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, ya samu karin darajar dukiya da ta kai dala miliyan dubu 30 da dala miliyan dari 2, a cewar rahoton da Bloomberg Billionaires Index ta fitar.
Rahoton ya bayyana cewa wannan karin daraja ya ɗaga matsayinsa zuwa na 75 a jerin mutanen da suka fi kowa arziki a duniya.
A baya ya kasance na 81 a jerin masu kudin duniya.
Dangote na da kaso mafi tsoka a kamfanin Dangote Cement Plc, wanda shi ne babban kamfanin samar da siminti a ƙasa da hamadar Sahara, kuma yana cikin kamfanonin da ake sayar da hannun jarinsu a kasuwar hannayen jari ta Najeriya.
Baya ga haka, Dangote ya mallaki babbar matatar man Fetur wacce itace mafi girma a Afirka, wato Dangote Refinery, wadda aka kaddamar da ita a ranar 22 ga Mayu, 2023.
Matatar wadda ke Ibeju-Lekki a jihar Legas, tana da kimar dala biliyan 20, kuma ita ce kadara mafi daraja da Dangote ke da ita.
Ya mallaki kashi 92 cikin 100 na hannun jarin matatar yayin da Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) ke da kashi 7 cikin 100.
Masana sun bayyana cewa, wannan sabon masana’anta ce ta taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka dukiyar Aliko Dangote a ‘yan watannin baya-bayan nan.
TST Hausa ta rawaito cewa har yanzy Elon Musk daga Amurika shine ke rike da kambun masu kudin duniya da yake da kudi dala biliyan 384 sai kuma Larry Ellison shima daga Amurika da ya zama na biyu da darajar kudi dala biliyan 383 sai mai shafin Facebook Mark Zuckerberg shima dan Amurika da yake kasancewa na uku da darajar kudi dala biliyan 264 biliyan.

