Limamin masallacin Juma’a na Usman Bn Affan a unguwar Gadon Kaya Sheikh Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya ya nemi al’ummar Musulmi su rika dagewa da yawaita tuba na gaske Inda yace , duk wanda ya saba neman gafarar Allah (istigfari), ba zai taɓa fāɗawa cikin halaka ba, domin istigfari na jawo rahamar Ubangiji da kare rayuwa daga matsalolin yau da Kullum.
Dr. Abdallah ya bayyana haka ne yayin hudubar da ya gabatar, a ranar Juma’a,mai taken, Istigifari hanyar warware matsaloli inda ya ce:
“Na rantse da Allah, mai yawan istigfari ba ya tabewa. Amma wanda ya mai da binciken laifin wasu abin yi, shi ne tababbe.”
Ya ce yin istigfari na goge zunubai kuma yana jawo albarka a rayuwa, sannan Yana yiwa gida da Iyali albarka,yana mai danganta hakan da maganar Allah Madaukakin Sarki a cikin Suratul Nuh, aya ta 10 zuwa 12, inda Annabi Nuhu (A.S) ya ce:
“Faqultu istaghfirū rabbakum innahu kāna ghaffārā
Yursili-s-samā’a ‘alaikum midrārā,
wa yumdidkum bi amwālin wa banīna wa yaj‘al lakum jannātin wa yaj‘al lakum anhārā.”
Ma’ana:
“Na ce ku nemi gafarar Ubangijinku, lallai Shi Mai yawan gafarane. Zai saukar muku da ruwan sama mai albarka, Ya ƙara muku dukiya da ‘ya’ya, Ya kuma sanya muku lambuna da rafuffuka.”
Dr. Abdallah ya kara da cewa, duk wanda ya mayar da neman laifin wasu aikin sa, ya manta da nasa, to shi ne tababben mutum, domin hakan na nuni da rashin hankali da rashin nutsuwa.
Ya shawarci al’umma su rika mai da hankali wajen gyara kansu, su yawaita istigfari da tuba domin samun rahamar Allah da zaman lafiya a rayuwa.
A cewarsa, duk wanda yake neman gafarar Allah da gaske, Allah ba zai taɓa barinsa cikin kunci ko matsala ba, domin kamar yadda Alƙur’ani ya tabbatar, istigfari hanya ce ta tsira, nutsuwa, da albarka.

