Gwamnatin Jihar Kano ta karbe gidajen da akayi watsi da su a birnin Kwankwasiyya tare da amincewa da ƙarin wa’adin zuwa ranar 31 ga Disamba, 2025, ga masu gine-gine tsakanin kashi 50 zuwa 95 cikin 100 na kammalawa, domin su samu damar kammala su kuma zauna cikinsu.
A wata Sanarwa da mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin yada labarai Hon. Ibrahim Adam ya fitar ya ce wannan mataki ya biyo bayan cikar wa’adin watanni shida da gwamnati ta bai wa masu gidaje domin su kammala gine-ginensu a cikin manyan biranen.
Gwamnatin ta kuma gargadi masu gine-gine da ba su nuna wata alamar ci gaba ba ko kuma suka bar filayensu babu aiki, cewa za a soke musu mallaka, gwamnati kuma za ta karɓi irin waɗannan gine-ginen, ta kammala su, sannan ta mayar wa da masu su kuɗin da suka biya.
Haka kuma, duk wani gini da aka yi ba bisa tsarin gine-ginen da aka amince da su ba a cikin waɗannan birane, za a rushe shi, domin kare inganci, tsaro da kyawun tsarin gine-gine na manyan biranen.
TST Hausa ta rawaito cewa kafin daukar matakin saida gwamnatin Kano ta sanar da masu gidaje a biranan biyu su tare domin gudun rasa gidajensu

