Wani Farfesa ɗan ƙasar Indiya mai suna VN Parthiban ya ɗauki hankalin duniya saboda hazakarsa a fannin karatu, inda ya mallaki takardun digiri sama da 150 a fannoni daban-daban.
Farfesan, wanda ke koyarwa a Jami’ar Madras da ke ƙasar Indiya, ya bayyana cewa dalilin da ya sa yake tattara digirori da shaidun karatu da yawa shi ne domin cika alkawarin da ya yi wa mahaifiyarsa, bayan ya bata mata rai lokacin da bai samu sakamako mai kyau ba a digirinsa na farko.
Ya ce tun daga wannan lokaci ya ɗaura niyya cewa ba zai daina karatu ba, har sai ya gamsar da mahaifiyarsa da kansa.
A halin yanzu, Farfesa Parthiban yana kashe kimanin kashi 90 cikin 100 na albashinsa wajen biyan kudin makaranta da sayen littattafai, domin ci gaba da karatu a fannoni daban-daban.
Abin mamaki, duk da yawan darussan da yake yi, Farfesan yana da dabarar tsara lokaci har yake iya halartar ajujuwa daban-daban lokaci guda. Wasu na bayyana cewa irin ƙwaƙwalwar da yake da ita sai an dinke saboda yadda yake iya riƙe bayanai masu yawa ba tare da mantuwa ba.
Sai dai tambayar da mutane da dama ke yi ita ce, shin Farfesa Parthiban yana amfani da duk waɗannan digirori ne a aikace, ko dai tattarawa yake don tarihi?

