Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kano, ta taya ɗan jarida Ahmed Mu’azu murnar samun nadin mukami a hukumar aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) a matsayin mataimakin shugaban sashen yaɗa labarai wato Technical Assistant (Media).
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Comrade Suleiman Abdullahi Dederi, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa wannan nadin da aka yi wa Ahmed Mu’azu, wanda ɗan asalin Jihar Kano ne, ya zama abin alfahari ga ‘yan jarida da ma al’ummar jihar baki ɗaya.
Sanarwar ta ce wannan ci gaba da aka samu na nuna yadda ake ƙara gane muhimmancin ƙwararru da jajirtattun ma’aikata a fannin yada labarai a ƙasar nan.
NUJ ta bayyana cewa Ahmad Mu’azu ya taɓa aiki a sashen hulɗa da jama’a na hukumar NAHCON, inda ya nuna hazaka da kwarewa wajen isar da saƙon hukumar ga al’umma.
Kungiyar ta kara da cewa tana da yakinin cewa gogewarsa za ta taimaka wajen ƙara inganta alaƙar hukumar da kafafen yada labarai, tare da bunƙasa hulɗa da jama’a.
A ƙarshe, NUJ ta taya shi murna tare da kira gare shi da ya ci gaba da zama abin koyi a fannin aikin jarida ta hanyar nuna gaskiya, kwarewa da jajircewa a duk inda yake aiki.

