Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa (NBC) da ta fadada ikon ta na sa ido zuwa kafafen rediyo da talabijin na yanar gizo, domin dakile yada labaran karya da maganganun da ke haddasa fitina a dandalin intanet.
Wannan kiran na cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran gwamna, Mustapha Muhammad, ya fitar.
Gwamna Yusuf ya yi wannan kiran ne a yayin jawabin da ya gabatar a taron Africast 2025 da hukumar NBC ta shirya a birnin Legas, inda masana harkar yada labarai, ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki suka tattauna kan sabbin abubuwa da ke tasowa a fannin watsa labarai.
A cewar Sanarwar gwamna Yusuf wanda darakatan yaɗa labaransa Hon. Sunusi Bature Dawakin Tofa, wakilita ,Gwamna Yusuf ya nuna damuwa kan yadda ake amfani da kafafen watsa labarai na yanar gizo wajen yada ra’ayoyi masu rarraba kawunan al’umma, musamman a bangaren addini da siyasa.
Ya gargadi cewa irin wadannan bayanai na iya zama barazana ga zaman lafiya, hadin kai da tsaron kasa.
“Kafafen yaɗa labarai na yanar gizo da ba su karkashin kulawa sun zama cibiyar yada labaran karya da maganganun batanci, musamman kan addini da siyasa”
Ayayin da yake mayar da martani, Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yada labarai ya yaba da wannan kira, yana mai bayyana cewa majalisar ta riga ta fara aiki kan gyaran dokar NBC, wadda ta kai matakin karatu na biyu a majalisar dattawa.
Ya ce wannan gyaran zai bai wa hukumar ikon kula da kafafen watsa labarai na yanar gizo da kuma tabbatar da cewa suna bin irin ka’idojin aiki da da’a kamar yadda ake bukata daga kafafen gargajiya.
Kiran da Gwamna Yusuf ya yi na daga cikin manufofin gwamnatinsa na ganin an samu kafafen yada labarai masu gaskiya, ilimin amfani da kafafen dijital, da kuma kare maslahar jama’a yayin da Najeriya ke ci gaba da daidaitawa da sabon tsarin watsa labarai na zamani.

