Gwamnatin Jihar Kano tayi alkwarin kammala manyan ayyukan gine-gine guda biyu wato gadar sama ta Tal’udu da ta Dan’Agundi kafin ƙarshen wannan shekara.
Kwamishinan ma’aikatar bibiyar ayyukan gwamnatin jiha Hon.Nura Iro Ma’aji ya bayyana hakan, inda ya ce ana gudanar da aikin ne da tsari mai karfi domin tabbatar da cewa an gama da inganci kuma akan lokaci.
Yace da zarar an kammala aikin Gadojin za’a kaddamar da fara amfani da su a watan Janairu na 2026 domin inganta tattalin arzikin jama’ar Kano da ma makota.
Rahotanni sun nuna cewa aikin gadar Tal’udu, zuwa yanzu ya kai kimanin kashi 60 cikin 100, yayin da gadar Dan’Agundi da ke da matakai uku ta kai kusan kashi 70 cikin 100 a halin yanzu.
A cewar kwamishinan, waɗannan manyan gadoji biyu waɗanda jimillar kuɗinsu ta kai Naira biliyan 27 za su taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa a cikin birnin Kano, tare da inganta tsarin zurga-zurgar jama’a.
TST Hausa ta rawaito cewa an fara aikin gadar Dan’Agundi ne a watan Disamba na shekara ta 2023, yayin da aikin Tal’udu shi ma aka fara shi a daidai wannan lokaci.
A baya an samu tsaiko ne saboda batun biyan diya.
Duk da haka, gwamnatin jihar ta ce tana da cikakken shiri domin ganin an kammala ayyukan kafin watan Disamba.
Wannan aikin na daga cikin manyan shirye-shiryen gwamnatin Kano na inganta ababen more rayuwa da rage cunkoson hanyoyi a birnin.

