Hukumar Wayar da Kan Al’umma ta Ƙasa (NOA) ta sanar da sabbin ka’idoji game da yadda za a rera taken ƙasa a taruka da shagulgulan gwamnati a faɗin ƙasar.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar , NOA ta bayyana cewa daga yanzu ana buƙatar a rera baitin farko kawai na taken ƙasa a dukkan tarukan gwamnati, maimakon baitoci uku gaba ɗaya da aka saba yi.
Sanarwar ta ƙara da cewa baitoci uku na cikakken taken ƙasa za a rera su ne kawai a lokuta na musamman kamar su:
Ranar ‘Yancin Kai (1 ga Oktoba),
Ranar Rantsar da Shugaban Ƙasa,
Ranar Tunawa da Sojoji (15 ga Janairu),
Ranar Dimokuraɗiyya (12 ga Yuni),
Ranar Rantsar da Majalisar Dokoki ta Ƙasa, da makamantansu.
Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan buƙatar daidaita yadda ake gudanar da taken ƙasa da kuma farfaɗo da al’adun kishin ƙasa a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman matasa.
NOA ta jaddada cewa wannan sabon tsarin zai taimaka wajen tabbatar da natsuwa, ladabi da girmamawa a yayin rera taken ƙasa a dukkan wuraren taro na gwamnati da na jami’ai.
TST Hausa ta rawaito cewa taken na Najeriya kafin bukatar rage tsayinsa ,yana Kai minti 1 dakika 50 (1: 50)

