Hukumar Kula da zurga zurgar ababen hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta ce ta hukunta direbobi da masu tuka adaidaita sahu guda tamanin da bakwai (87) da suka karya dokokin zurga-zurga a cikin birnin Kano.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Malam Abubakar Ibrahim Sharada ya fitar yace an gudanar da shari’ar ne a kotunan tafi da gidanka da aka kafa domin rage yawaitar masu karya dokar hanya da kuma tabbatar da tsari da bin doka a titunan Kano.
Rahoton hukumar ya nuna cewa a cikin kwanaki biyu da suka gabata, an gudanar da zaman kotuna a wurare daban-daban a cikin birnin, inda aka yanke hukunci ga masu laifin da aka kama suna wucewa alhalin an tsadar da su da kuma yin wasu abubuwa da suka sabawa dokokin hanya.
Ɗaya daga cikin kotunan da ta gudanar da zama a kusa da mahadar titin Magwan a kan titin gidan gwamnati ta hukunta mutane arba’in da ɗaya (41) karkashin jagorancin Alkalin Babbar Kotu, Hajiya Halima Wali.
Haka kuma wani zama da aka gudanar a kan hanyar zuwa jami’ar Bayero kusa da Kofar Famfo karkashin Alkali Hauwa Abba, ya hukunta mutane arba’in da shida (46) da suka haɗa da direbobi da masu tukin adaidaita sahu.
Da yake magana kan lamarin, Manajan Darakta na KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da zaman kotunan tafi da gidanka a sassa daban-daban na birnin Kano, domin dakile masu take dokar danjar tituna.
Ya ce:
“Wannan mataki ba don tsoratar da direbobi ko masu tuka adaidaita sahu ba ne, sai don tabbatar da bin doka da tsari a tituna, da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma, bisa manufofin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.”In ji Sanarwar.
Faisal Mahmud ya kuma yaba da ƙwazon Alkalai da jami’an tsaro da ke aiki tare da tawagar KAROTA wajen aiwatar da wannan aiki, yana mai cewa jajircewarsu da kishin aiki ne ya taimaka wajen samun nasarar da aka samu.

