Gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta ce har yanzu babu wani ɗan fursuna da aka amince da shi cikin jerin masu afuwar shugaban ƙasa da aka saki daga gidan yari, domin aikin yana cikin matakin duba na ƙarshe.
Babban Lauyan gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ne ya bayyana haka, inda ya ce ana ci gaba da sake nazari da tantance jerin sunayen kafin a fitar da takardun sakin su.
A cewarsa, ko da majalisar koli ta amince da jerin sunayen, akwai wani mataki na ƙarshe da ake sake dubawa domin gyara ko sauya wasu bayanai kafin a fitar da takardun afuwar daga fadar shugaban ƙasa.
Fagbemi ya ce wannan mataki yana daga cikin tsarin gudanar da aikin afuwar domin tabbatar da cewa an bi duk ka’idojin doka da tsari kafin sakin kowane ɗan fursuna.
Rahotanni sun nuna cewa wannan bayani na gwamnati na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan jerin sunayen da aka ruwaito, ciki har da zargin saka wasu da ake tuhuma da manyan laifuka kamar kisa da safarar miyagun ƙwayoyi, da kuma batun cewa an saka sunan Maryam Sanda cikin jerin.
Gwamnati ta jaddada cewa aikin bayar da afuwar shugaban ƙasa yana ƙarƙashin duba da sake nazari, kuma jerin na iya sauyawa kafin a fitar da sakamako na ƙarshe.
