Gwamnatin jihar Kano ta gargadi malaman makarantun Islamiyya da na Al-Qur’ani mai girma da su daina koyar da ɗalibai cikin murtukewar fuska ko kuma yawaita wasa a lokacin darasi, domin hakan na iya hana ɗalibai fahimtar abin da ake koya musu.
Kwamishina na biyu a hukumar, shari’a ta jihar Kano Sheikh Ali Ɗan Abba, ne ya bayyana hakan a ofishinsa lokacin da yake karɓar rahoton bincike daga Majalisar Makarantun Islamiyya da na Al-Qur’ani mai girma, kan hanyoyin gyara tsarin koyarwa a makarantun Islamiyya a fadin jihar.
Sheikh Ɗan Abba ya ce shugaban hukumar Shari’a ta Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ya ɗauki wannan mataki ne bayan lura da nakasu daban-daban da ake samu wajen koyar da ɗalibai, inda hukumar ke ƙoƙarin ganin an inganta tsarin koyarwar.
Ya bayyana cewa amfani da sabbin dabarun koyarwa a makarantun Islamiyya zai taimaka wajen inganta tarbiyyar ɗalibai da kuma rage yawaitar matsalolin da ke addabar matasa, irin su faɗan daba, fashin waya, ɗaukar makamai da shaye-shaye.
Sheikh Ɗan Abba ya ƙara da cewa, “ya kamata malamai su guji koyarwa cikin fushi ko murtukewar fuska, su kuma rika amfani da dabaru cikin raha domin sa ɗalibai su fi gane darussa cikin sauƙi.”
A nasa jawabin, shugaban Majalisar Makarantun Islamiyya da na Al-Qur’ani mai girma a Jihar Kano, Mallam Sani Umar Mika’il, ya gode wa hukumar Shari’a bisa amincewa da binciken da suka gudanar cikin makonni uku.
Ya kuma yi kira ga malaman makarantun da su bada haɗin kai wajen aiwatar da sabuwar manhajar koyarwa domin samar da ingantaccen ilimi da tarbiyya ga ɗalibai.
A lokacin da Sheikh Ali Ɗan Abba ke karɓar rahoton, yana tare da Kwamishina na ɗaya, Gwani Hadi Ɗahiru Yakasai, tare da wasu daraktocin hukumar.

