Farfesa Mansur Sokoto, malamin addini kuma masanin ilimin tauhidi, ya bayyana cewa bai dace da koyarwar addinin Musulunci mutum ya yafe hakkin wani da aka zalunta ba, domin hakan shiga hurumin Allah ne.
A cewarsa, hakkin bawa abu ne da Allah ba ya yafewa sai dai wanda aka zalunta ya amince ko kuma a bi shi da adalci ta hanyar hukunci.
Ya ce duk wanda ya yi ƙoƙarin yafe hakkin wani da ba nasa ba, to kamar ya tsallaka iyakar da Allah ya gindaya ne.
Farfesa Mansur ya yi wannan bayani ne yayin da yake tsokaci kan batun yafiyar da ake ta tattaunawa a kafafen yada labarai, musamman bayan yadda ake samun rahotanni na mutane da ke neman a yafewa masu laifi da suka cutar da wasu.
Ya ƙara da cewa: “Musulunci addini ne na adalci, ba na tausayi da son kai ba. Idan mutum ya kashe wani ko ya zalunce shi, ba wanda yake da ikon yafe masa face wanda aka zalunta. In ba haka ba, wannan shiga hurumin Allah ne.”
Farfesan ya kuma yi kira ga shugabanni, malamai da al’umma su rika yin taka-tsantsan wajen bayar da ra’ayoyi a kan irin wadannan lamurra, don kada a karkatar da fahimtar jama’a daga ainihin koyarwar addinin Musulunci.

