Ƙwararren masani akan sauyin yanayi da muhalli a Najeriya Farfesa Aliyu Baba Nabegu ya bayyana cewa ruwan sama da ake ta samu a watan Oktoba ba al’ada ba ce ta damuna, yana nuna cewa Duniya na fama da rashin lafiya sakamakon sauyin yanayi.
Farfesa Nabegu ya bayyana haka ne yayin zantawarsa da TST Hausa a taron masana ilimin Ƙasa wato Geography da aka gudanar a Kano (ANG 2025)
Farfesa Nabegu wanda shine maibaiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin sauyin ya ce sauyin yanayi (climate change) ne ya haddasa wannan yanayin ruwan sama bayan wucewar damina.
A cewarsa, a da, ruwan sama kan tsaya tun farkon watan Satumba a yawancin yankunan Najeriya musamman Arewa da suke samun ruwan sama sau daya a shekara, amma a yanzu ana cigaba da samun ruwan sama har zuwa tsakiyar watan Oktoba, wanda hakan ke nuna cewa muhalli na cikin wani hali na lalacewa.
“Ruwan sama bayan damina alama ce ta cewa duniya ba ta cikin koshin lafiya. Abubuwan da ɗan Adam ke aikatawa kamar sare dazuka, kona filaye, da gurbata iska suna taimakawa wajen lalata tsarin yanayi,” in ji Farfesa Nabegu.
Yace idan akayi la’akari da yadda ruwan sama ya sauka da wuri a damunar bana ya nuna cewa duniya na fama da matsalolin sauyin yanayi.
Ya bukaci ’yan Najeriya da su nemi hanyoyin kare muhalli, ta hanyar dasa bishiyoyi, rage amfani da kwal da filastik, da gujewa kona shara a fili, domin rage illolin sauyin yanayi da ke barazana ga rayuwar ɗan Adam.
Farfesa Nabegu ya kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su ƙara ɗaukar matakan kare muhalli, tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin kula da yanayi domin kare lafiyar al’umma da dorewar rayuwa.

