An zaɓi Farfesa P. O. Phil-Eze daga Jami’ar Najeriya Nsukka (UNN) a matsayin sabon shugaban ƙungiyar masana ilimin Ƙasa wato Association of Nigerian Geographers (ANG).
Zaɓen ya gudana ne a lokacin taron shekara-shekara na ƙungiyar da aka gudanar a ranar Talata, 7 ga Oktoba, 2025 a birnin Kano.
Farfesa Phil-Eze, wanda fitaccen malami ne a sashen ilimin ƙasa (Geography Department) na Jami’ar Najeriya Nsukka, yana daga cikin manyan masana da suka yi fice a fannin tsarrai da halittun Ƙasa wato biogeography,da Ilimi ruwan koramu wato hydrology, da nazarin muhalli.
Ya taɓa rike mukamin shugaban sashen ilimin ƙasa na jami’ar, haka kuma yana cikin masu fafutukar kare muhalli da raya ilimin ƙasar Najeriya.
A cewar wasu mambobin ƙungiyar, zaben Farfesa Phil-Eze ya biyo bayan kammala wa’adin tsohon shugaban ƙungiyar, Farfesa Sani Abubakar Mashi inda aka bayyana cewa sabon shugaban na da ƙwarewa da hangen nesa wajen jagorantar ƙungiyar zuwa sabon matsayi.
TST Hausa ta rawaito cewa a bana a karon farko jami’ar Northwest dake Kano ita ce ta karbi bakuncin babban taron Kungiyar ta ANG na bana.
A ganawarsa da manema labarai Shugaban sashen nazarin ilimin Ƙasa na jami’ar Northwest Dr.Nazifi Umar Alaramma ya ce zaɓen ya gudana cikin lumana tare da halartar manyan malamai daga sassan ilimin ƙasa na jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar.
Ya ce ana tsammanin sabon shugaban zai mayar da hankali kan haɓaka binciken kimiyya,da haɗa kai tsakanin jami’o’i, da kuma samar da damar tattaunawa tsakanin masana ƙasa da masu tsara manufofin gwamnati domin inganta harkokin ci gaban muhalli a Najeriya.

