Majalisar Koli ta Ƙasa ta amince da nadin Farfesa Joash Ojo Amupitan daga jihar Kogi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Rahoton ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai mika sunan Farfesa Amupitan ga Majalisar Dattawa domin tantancewa da kuma tabbatar da nadin nasa a hukumance.
Sai dai, zuwa yanzu babu wata tabbaci daga manyan kafafen yada labarai na ƙasa ko kuma daga hukumar INEC kan wannan sabon nadin.
Ana tunawa cewa wa’adin Shugaban INEC na yanzu, Farfesa Mahmood Yakubu, zai ƙare a watan Oktoba na shekarar 2025, inda ake sa ran gwamnati za ta tabbatar da sabon shugaban kafin ƙarshen wa’adin nasa.
Idan kuwa hakan bai faru ba, ana tsammanin kwamishina mafi girma a hukumar zai rike mukamin na wucin gadi har zuwa lokacin da za a tabbatar da sabon shugaban hukumar

