Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da hada almundahana ta Kasa (ICPC) ta ce za ta gurfanar da wani dan Jarida mai suna Alkazim Kabir, wanda ake kira da Abbati Kabiru Abuwa, da ke Kano, bisa zargin aikata damfara da ta kai kimanin naira miliyan 14.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Demola Bakare ya fitar a ranar Laraba,yace an yanke shawarar gurfanar da wanda ake zargin ne bayan karɓar korafe-korafe da dama daga jama’a, inda aka zarge shi da yin damfara, da yiwa jami’an gwamnati sojan gona da kuma yaudara.
Binciken hukumar ICPC ya gano cewa, Kabir ya sha yin sojan gona da sunan shi wani babban jami’an gwamnati ne ciki har da kiran kansa a matsayin hadiman shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa, da kuma wasu ‘yan majalisar tarayya, domin damfarar mutane.
Wanda ake zargin ya karɓi dala 3,300 da Riyal 1,620 daga wasu mutane biyu, inda ya bayyana musu cewa yana aiki a matsayin hadimin fadar shugaban kasa.
Hukumar ta kuma gano cewa wanda ake zargin ya kware wajen karɓar kuɗi da kaya ta hanyar zamba, musamman ta hanyar amfani da damar da ke tattare da shirye-shiryen tafiya zuwa ƙasashen waje domin ibada.
A lokacin da ya tafi aikin Umrah a ƙasar Saudiyya, ana zargin ya karɓi Riyal 11,000 daga wani abokin tafiya, sannan daga baya ya turo masa da takardar bogi ta canja wajen kuɗin domin nuna cewa ya biya bashin.
Haka kuma, ya aika wa wani dillalin kula da masu tafiye tafiye da takardar ƙarya ta canja wurin kuɗi na Naira miliyan 3 da dubu dari biyu wanda ya ce ya biya kudin jirgi, da otel da jirgin ƙasa.
Hukumar ICPC ta ce an riga an shigar da ƙarar wanda ake zargi a kotu, kuma za a gurfanar da shi gaban kotu mai hurumi nan bada jimawa ba, da zarar an sanya ranar zaman shari’ar.

