Gwamnatin jihar Kano ta nuna damuwa da takaici kan yadda ake gwaranci a rubutun Hausa a jikin allunan tallace tallace da ake kafewa a gefen manyan titunan jihar Kano.
A zantawarsa da Jaridar TST Hausa, daraktan wayar da kan jama’a na hukumar kula da allunan tallace tallace da dangoginsu ta jihar Kano, Munzali Muhammad Hausawa,yace hankalin hukumar yaje kan yadda ake cece kuce game da wani rubutun Hausa da ba’a yi daidai ba ya dauki hankalin jama’a har wani matashi ya kai korafi.
Yace abinda jama’a ba su sa ni ba ,shi ne hukumar su bata da hurumin daukar mataki akan irin wannan batu ,ita kawai tana kula da allunan da ake makalaawa ne amma ba rubutun da ke jikin allo ba.
Munzali Muhammad yace akwai hukuma guda ta kula da dokokin tallace tallace wato Advertisement regulatory council of Nigeria (ARCON ) da ke kula da wannan bangaren.
Daraktan yace su kansu suna mutukar damuwa akan abinda ake na rubutun gwaranci a kan allunan tallace tallace.
TST Hausa ta rawaito cewa wani matashi Ahmad Khamis Kibiya a Kano shi ne tunda farko ya rubuta ƙorafi ga kamfanin Moniepoint kan fassarar Hausa mara daidaito da aka yi a ɗaya daga cikin allon tallan kamfanin da ke Naibawa ƴan Katako, Zaria Road, a jihar Kano.
A cewar matashin, fassarar da aka rubuta a kan allon bata wakilci harshen Hausa yadda ya dace ba, kuma ta nuna rashin amfani da ƙwararren mai fassara wajen shirya tallan.
Ya bayyana cewa wannan kuskuren abin damuwa ne musamman ga jihar Kano, wadda ake kallon ta a matsayin cibiyar harshe da al’adun Hausawa a Afirka, inda miliyoyin Hausawa ke zaune.
A cikin ƙorafinsa, matashin ya bukaci kamfanin Moniepoint da ya dauki matakan gyara cikin gaggawa ta hanyar:
Ya ce irin wannan kuskure na iya zama abin tozarci da raini ga al’ummar Hausawa, musamman ganin yadda kamfanin Moniepoint ke da karɓuwa a fannin hada-hadar kuɗi a Najeriya.
Hukumar tace bayan yaɗa lamarin a shafukan sada zumunta, jama’a da dama sun nemi a dauki mataki akan kamfanin da ya kafa allon tallan.

