Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce tun daga lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki a shekarar 2023,har zuwa yau ba ta taba satar filin makaranta, ko makabarta, ko wani fili da aka ware domin amfanin al’umma ba.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin wani taro da kungiyar naɗaɗɗun kansiloli da masu baiwa shigabannin kananan hukumomi shawara na jihar Kano a gidan gwamnatin Kano.
TST Hausa ta rawaito cewa naɗaɗɗun kansiloli da masu baiwa shigabannin kananan hukumomi shawara sun Kai 747.
Gwamnan ya ce gwamnatin sa ta kuduri aniyar kare dukkan kadarorin gwamnati da na al’umma daga masu son mallake su ta hanyoyi marasa kyau.
Ya ce, “Tun da muka hau mulki, ba mu taba satar filin makaranta ko makabarta ba. Muna tabbatar muku da cewa zamuyi duk mai yiyuwa domin ganin an dawo da duk wani fili da aka karbe ba bisa ka’ida ba a gwamnatin baya.
Gwamnan ya kuma shaida cewa a shirye ya ke ya cigaba da tallafawa nadaddun kansilolin ,kamar yadda ya tallafawa zababbun kansilolin Kano.
Gwamna Yusuf ya kara dacewa zai samu lokacin domin baiwa naɗaɗɗun kansilolin da masu baiwa shigabannin kananan hukumomi shawara horo na musamman domin sanin makamar aiki.
Ya kuma bukace su da su cigaba da bayar da hadin kai ga gwamnatinsa wajen gudanar da ayyukan ci gaban jihar, tare da fadin gaskiya idan aka ga wani laifi a cikin tsarin gwamnati.

