Masana ilimin ƙasa a Najeriya sun bayyana muhimmancin ilimin Geography wajen magance matsalolin da suka shafi cigaban ƙasa, yayin taron shekara-shekara na ƙungiyar masana ilimin Ƙasa ta Najeriya wato Association of Nigerian Geographers (ANG) karo na 65, da ake gudanarwa jami’ar Northwest da ke a Jihar Kano.
Taron, wanda ya hada kan masana sama da 500 daga jihohin Najeriya daban daban a kalla masu gabatar da mukala 250 ne zasu gabatar da sakamakon binciken da su kayi.
Taron zai mayar da hankali kan yadda ilimin ƙasa zai iya taka rawa wajen rage bambancin tattalin arziki, da kuma inganta daidaiton zamantakewa a ƙasashe masu tasowa.
A jawabinsa na bude taron, Shugaban jami’ar Northwest Farfesa Mukatar Atiku Kurawa ya bayyana cewa ilimin Geography da nazarin yanayin sararin ƙasa (spatial analysis) na da muhimmanci wajen gano da kuma shawo kan matsalolin muhalli,da tattalin arziki, da zamantakewa da ake fuskanta a kasahen duniya.
A Jawabinsa na maraba, Shugaban sashen nazarin ilimin Ƙasa na jami’ar Northwest Dr. Nazifi Umar Alaramma ya ce babban fatansu shi ne warware matsalolin Najeriya anan gaba.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati,da shugabannin jami’o’i, malamai, da kwararru daga sassa daban-daban na ƙasar.
Shugaban Kungiyar ta ANG Farfesa Sani Abubakar Mashi ya ce an shirya zaman tattaunawa,da gabatar da takardu, da nune-nunen bincike, domin zurfafa nazari kan matsalolin da ke shafar ci gaban ƙasashe masu tasowa da hanyoyin magance su ta hanyar amfani da ilimin Geography.

