Hukumar kula da yiwa Malaman makaranta rijista ta Najeriya (TRCN) ta bayyana damuwa kan yawaitar malamai marasa cancanta da ke koyarwa a makarantu a fadin Najeriya musamman a makarantun masu zaman kansu.
Shugabar hukumar, Dr.Ronke Soyombo ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai, inda ta ce rashin samun malamai masu kwarewa da shaidar cancanta na daga cikin manyan dalilan da ke haddasa raguwar ingancin ilimi a Najeriya.
A cewarta, binciken hukumar ya gano cewa yawancin malamai marasa takardar cancanta na koyarwa ne a makarantun ‘yan private, abin da ke kawo cikas ga kokarin gwamnati na inganta ilimi.
Domin magance matsalar, TRCN ta kaddamar da wani shirin horaswa na gaggawa domin bai wa malamai damar samun cancantar zama cikakkun malamai ta hanyar Diploma na Musamman a fannin Koyarwa (Professional Diploma in Education).
Haka kuma, hukumar ta samar da shirin horaswar watanni shida ga malamai da ke da gogewa a fannin koyarwa amma ba su da takardar ilimi, domin su samu cancantar doka ta TRCN.
Hukumar ta ce tana kuma kokarin inganta fannin koyarwa ta hanyar bunkasa kwarewar malamai, samar da kayan aiki, da karfafa hadin kai tsakaninsu wajen tsara darussa da hanyoyin koyarwa domin tabbatar da ingancin ilimi.
TRCN ta roki gwamnati da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da su kara tallafawa malamai masu cancanta, domin tabbatar da cewa ‘ya’yan Najeriya suna samun ilimi nagari da ya dace da zamani.

