Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da kashe kuɗi naira miliyan dubu 1 da miliya dari 6 domin shirya auren zawarawa a fadin jihar karo na biyu.
Wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnatin sa na taimaka wa mata da maza masu neman aure, musamman wadanda suka rasa mazajensu ko matayensu, domin farfado da martabar aure da inganta rayuwar al’umma.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya shi ne ya bayyana hakan bayan kammala zaman majalisar zartaswar jihar karo na 32 wanda gwamna Yusuf ya jagoranta.
TST Hausa ta rawaito cewa zaman majalisar zartaswar ya amince da kashe kuɗi sama da naira miliyan dubu 45 da miliyan dari 6 domin gudanar da ayyuka na musamman da kuma samar da kayan more rayuwa da bangaren samar da ruwan sha da lantarki da Jin kai da samar da tituna da bangaren cigaban ilimi da tsaro da sauransu.
Rahotanni sun nuna cewa, gwamnatin jihar ta ware kuɗi don sayen dakin ma’aurata da,biyan kudin sadaki da kuma shirya bukukuwan aure ga waɗanda suka cancanta, karkashin kulawar Ma’aikatar Harkokin addinai ta jihar Kano.
Kwamishinan ya kara dacewa manufar shirin shi ne rage yawaitar zawarawa da marasa aure, tare da ƙarfafa zumunci da zaman lafiya a cikin al’umma.
Ya kuma yi kira ga wadanda za su amfana da shirin da su nuna gaskiya da biyayya, tare da amfani da damar wajen gina kyakkyawar rayuwar aure.

