Gwannatin jihar Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga duk wani wa’azi a Kano
Sakataren Majalisar Shura ta Jihar Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya bayyana cewa an dakatar da Malam Lawan Triumph daga ci gaba da gudanar da wa’azi a fadin jihar ne bayan karɓar Rahoton akan takaddamar da ta taso akansa
A cewar sanarwar da majalisar ta fitar, an ɗauki wannan mataki ne domin bawa Malam Lawan damar bayyana a gaban majalisar, inda zai yi karin bayani da kuma kare kansa kan zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Majalisar ta ce dakatarwar na da nufin tabbatar da adalci da tsare mutuncin addini, tare da baiwa Malam Lawan damar yin tsokaci kai tsaye kan zarge-zargen kafin daukar mataki na gaba.

