Kungiyar Ma’aikatan Manyan Harkokin Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta umarci rassanta a fadin kasar nan da su dakatar da isar da iskar gas zuwa kamfanin NGIC tare da daina jigilar danyen mai zuwa matatar man Dangote daga ranar 26 ga Satumba, 2025.
Masana sun bayyana cewa wannan matakin na iya jawo cikas ga samar da man fetur, dizal, kerosene, iskar gas na girki da kuma man jiragen sama. Bugu da kari, rikicin na iya zama barazana ga jarin kasashen waje da kudaden shiga na gwamnati.
Kungiyar ta PENGASSAN ta yi gargadin cewa wannan ba wata doka ba ce, don haka ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta shawo kan matsalar domin gujewa tashin hankali da kare al’ummar kasa.
Rahotanni sun nuna cewa idan rikicin ya ci gaba ba tare da an warware shi ba, akwai yiwuwar a fuskanci karancin man fetur a kasuwanni, wanda hakan zai iya haddasa karin farashi da kara jefa al’umma cikin matsin tattalin arziki.

