Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, a matsayin ranar hutu domin bikin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka..
Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a wata takardar manema labarai da ya fitar, inda ya taya ’yan Najeriya murnar wannan rana mai muhimmanci.
Ya bayyana cewa bikin zagayowar ranar samun ’yancin kai ya zama lokaci na tunawa da sadaukarwar da aka yi wajen samun mulkin kai, tare da ƙarfafa al’umma su ci gaba da zama cikin haɗin kai da zaman lafiya.
Tunji-Ojo ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan rana wajen tunawa da muhimmancin haɗin kai da kishin ƙasa, domin ci gaban al’umma da ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya.
Najeriya ta samu ’yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka a ranar 1 ga Oktoba, 1960, kuma a bana tana cika shekaru 65 da wannan tarihi mai muhimmanci.

