Gwamnan Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da gina kasa mai hadin kai da ci gaba ta hanyar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar da kasa baki daya.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne a yayin wani taron lacca da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida karkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ta shirya a Kano.
An shirya taron ne a wani bangare na bikin ranar samun yancin Najeriya shekara 65 daga Turawan mulkin mallaka.
Za’a gudanar da taron ne a ranar laraba 1 ga watan Oktoba na shekarar 2025.
Gwamna Yusuf wanda Shugaban ma’aikata na fadar gwamnati Dr.Sulaiman Wali Sani Mni ya wakilta ya ce tsaro shi ne ginshikin duk wani cigaba, domin babu abin da za a iya cimmawa ba tare da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.
“Ya kamata kowa ya dauki tsaron kasa a matsayin hakkin kowa da kowa, ba wai na gwamnati kawai ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa gwamnatinsa na aiki tare da hukumomin tsaro, da shugabannin gargajiya da na al’umma domin ƙarfafa zaman lafiya da hadin kai.
Ya ce shirye-shiryen karfafa lwa matasa,guiwa ta hanyar koyar da su sana’o’i da habaka ilimi na daga cikin muhimman matakan da ake dauka wajen magance tushen matsalolin tsaro.
“Ta hanyar wadannan shirye-shirye, muna rage dalilan da ke jawo rashin tsaro tare da samar da damammaki ga matasanmu domin su taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma,”acewar Gwamna Yusuf.
Haka kuma, gwamnan ya yabawa ma’aikatar Yaɗa labarai da harkokin cikin gida karkashin jagorancin Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya saboda shirya wannan lacca da kuma fito da muhimmancin shirin Save Corridor na dakile shaye shayen miyagun kwayoyi da kwacen waya a jihar.
Ya ce wannan shiri, wanda ya mayar da hankali kan gyara da sake shigar da wadanda suka tuba cikin al’umma, ya dace da manufar gwamnatinsa ta inganta sulhu, hadin kai da ci gaban jama’a.
Anasa jawabin kwamishinan ma’aikatar yaɗa labarai ta Jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya godewa mahalarta taron tare da shaida cewa an shirya shi ne domin zaburar da matasa mahimmacin kaunar jiharsu da kishin kasa .
Sannan yace taron wata hanya ce ta jan matasa a jika da Kuma nuna mahimmacin riko da al’adun yankin da mutum ya fito.

