Limamin masallacin Juma’a na Usman Bn Affan dake kofar Gadon Kaya a karamar hukumar Gwale Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya, ya bayyana cewa duk da irin matsaloli da tsanani da ake fuskanta a rayuwa, malamai da al’umma ba za su daina koyar da karantar da Tauhidi ba, domin shi ne ginshiƙin Musulunci da tushen imani.
TST Hausa ta rawaito cewa hudubar mai take Tauhidi shi ne tushen zama lafiya,hakan na nufin yaki da shirka da duk wani abu da zai kawo cikas a karantarwar da Malamai keyi na kadaita Allah shi kadai a bauta da kuma baiwa Annabi Muhammad SAW duk wata kariya da matsayin da addini ya bashi da karama da girmamawa.
Dr. Abdallah ya yi wannan jawabi ne a cikin hudubar da ya gabatar a ranar Juma’a ta yau 26 ga watan Satimba 2025, inda ya jaddada cewa wajibi ne ga malamai da masu ilimi su dage wajen yada darussan Tauhidi a kowane lokaci, domin tsare al’umma daga karkacewa zuwa ga shirki da bidi’a.
Ya ce:
Komai rintsi da wahalhalu, ba za mu daina karantar da Tauhidi ba. Domin shi ne hasken Musulunci, kuma shi ne abin da ya bambanta Musulmi da sauran addinai. Duk wanda ya rasa Tauhidi, imanin sa ya zama cikin hadari”In ji Malamin.
Malamin ya kuma bayyana cewa koyar da Tauhidi ba wai kawai ya ke tabbatar da tsarkin akida ba ne, har ma yana taimakawa wajen daidaita halaye, ƙarfafa zumunci da kuma tabbatar da gaskiya a cikin al’umma.
Haka kuma, ya yi kira ga ɗalibai da iyaye da su ƙara dagewa wajen halartar darussa da tarurrukan ilimi, musamman na Tauhidi, yana mai jaddada muhimmancin samun malamai nagari da za a dogara da su wajen koyon ilimi na gaskiya.
Wani ɗalibi da ya halarci hudubar, ya shaidawa TST Hausa jin daɗinsa da wannan kira, yana mai cewa: “Hudubar ta ba mu ƙwarin gwiwa mu ci gaba da bin sahun malamai domin samun ilimi mai amfani da zai tsare imaninmu”
Dr. Abdallah Gadon Kaya ya ƙara jan hankali da cewa: “Al’umma ba za ta samu ci gaba da zaman lafiya ba tare da ilimi na Tauhidi ba. Idan aka yi watsi da shi, za a rasa ginshiƙin Musulunci, kuma hakan zai haifar da barazana ga rayuwar addini da ta duniya.
Hudubar ta sa da alama Raddi ne akan yadda wasu ke ta kiraye kiraye domin hukunta malamin Addinin musulunci, Shiek Lawan Abubakar Triumph Wanda suke zarginsa da kalaman batanci ga Addinin musulunci.
Dr. Abdullah Usman Gadon Kaya ya nemi mahukunta da hukumomin tsaro da gwamnatin Kano su yi takatsantsan akan abinda ake zargin malamin.
Ya ce kamata ya yi a rika barin Malamai masana addini sosai suna nazari akan duk wani da ake zargi da batanci a cikin abinda ya shafi karantarwa.
Malamin yace ba daidai ba ne a rika barin sha’anin Addinin musulunci a hannun marasa Ilimi.

