Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta karɓi koke-koke da ƙorafe-ƙorafe daga kungiyoyin addini kan kalaman da Sheikh Lawan Triumph ya yi a kwanan nan kan fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ba da umarnin a mika batun ga Majalisar Shura ta Jiha domin ta yi nazari tare da ba da shawarwari.
Mai magana da yawun ofishin Sakataren Gwamnati na Jiha, Musa Tanko, ya bayyana cewa kungiyoyin da suka shigar da koke-koken sun haɗa da Safiyatul Islam of Nigeria,da Kungiyar Wayar da Kan Matasa ta Tijjaniyya,da Interfaith Parties for Peace and Development,da Sairul Qalbi Foundation,da Habbullah Mateen Foundation,da Limaman Masallatan Juma’a na Qadiriyya, da Kwamitin Malaman Sunnah Kano da kuma Multaqa Ahbab Alsufiyya.
Sakataren Gwamnati na Jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya tabbatar da cewa gwamnati ta mika batun ne domin a yi masa cikakken nazari da kuma bayar da shawarwarin da suka dace.
Ya ce gwamnati na da cikakken niyyar tabbatar da zaman lafiya,da haɗin kai da mutunta juna tsakanin kungiyoyin addini a jihar.
“Mun yi kira ga jama’ar Kano da su kwantar da hankali, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum tare da bin doka da oda,” in ji shi.
TST Hausa ta rawaito cewa a ranar laraba ne wasu matasa sukayi zanga zanga kan furucin malamin akan Manzon tsira Annabi Muhammad SAW da suka ce sunyi tsauri.
Daga nan gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya karbi korafin matasan yace su rubuta a mikawa ofishin Sakataren gwamnatin jiha.
Saidai a safiyar Alhamis suma wasu Malaman Ahalussunnah karkashin jagorancin Dr.Abdullah Gadon Kaya ,su ka mika nasu koken cewa Malamin yana kan daidai,kuma suna bukatar ayi adalci

