Kungiyar Mahaddatan Alkur’ani ta Najeriya wato (Center for Qur’anic Reciters Nigeria) ta bayyana cewa bata da hannu kuma bata amince da nadin da aka yiwa tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin Khadimul Qur’an, tana mai bayyana lamarin a matsayin mataki da ya saba ka’idoji kuma haramtacce ne.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai na kasa, Gwani Sadiq Minna, ya fitar a Kano, kungiyar ta ce wasu mutane ne suka yi amfani da sunanta wajen shirya wannan nad’i ba tare da izini ko yardar shugabancin Mahaddatan Alkur’ani ba.
Ƙungiyar ta ce nadin da aka yiwa Ganduje na bogi ne.
TST Hausa ta rawaito cewa a karshen makon da ya gabata ne wasu daga cikin yan Kungiyar mahaddata Al’qurani ta kasa ta nadawa Ganduje rawani a matsayin Kadimul Qur’an.
Kungiyar Mahaddatan Alkur’ani karkashin jagorancin Goni Sunusi Abubakar bata taba amincewa da amfani da sunanta wajen nada tsohon Gwamnan Kano a matsayin Khadimul Qur’an ba.
Wannan abu ya saba tsari, kuma mun nesanta kanmu daga cikinsa gaba ɗaya,” in ji sanarwar.
Kungiyar ta yi gargadi ga duk wanda ke amfani da sunanta wajen raba kan al’umma da haddasa rikici, tare da bayyana cewa ma hukumomin tsaro a Jihar Kano sun nuna rashin amincewa da wannan shiri.
Haka kuma, ta yi kira ga malamai, mahaddata da masoya Alkur’ani da su yi watsi da wannan batu, tare da guje wa duk wani rikici ko rudani da ka iya tasowa.
A karshe, kungiyar ta jaddada matsayinta da cewa “bamu da masaniya, bamu amince ba, kuma ba za mu taɓa kasancewa tare da wadanda suka kulla wannan lamari ba.”
ABIN LURA
A wani bin diddigi da TST Hausa ta yi ta gano cewa,wani tsagi ne daga cikin Kungiyar ta karrama Dr. Ganduje yayinda daya tsagin da suke rigima da juna suka nesanta kansu.
Shugabancin da ake zargin sun nesanta kansu da nadin Ganduje Kadimul Qur’an suna da babban ofishinsu ne na kasa a birnin dake Gusau dake Jihar Zamfara ,sai kuma daya tsagin da suka ce watakila anyi amfani da takardar su ta Kungiya an rubuta labarin kuma wadanda suma wasu can daban suka naɗa Ganduje da sunansu ,suna da babban ofishinu ne a Zaria.

