Shugaban Ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ya taya uwargidansa Sanata Oluremi Tinubu, murnar zagayowar ranar haihuwarta ta 65.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Shugaban Ƙasan ya bayyana Oluremi a matsayin “soyayyarsa ta rayuwa” da kuma “ginshiƙin kwanciyar hankalinsa,” yana mai yabawa da rawar da ta taka a tsawon shekarun gwagwarmayarsa da siyasa.
“Oluremi na, yayinda kike bikin cika shekara 65 a yau, ina girmama mace wadda ƙarfin zuciya da kwantar da hankalinta suka kasance tushen ƙarfin guiwana,in ji Tinubu.
TST Hausa ta rawaito cewa Tinubu yace daga shekaru na gwagwarmaya da gudun hijira, har zuwa yau da nake jagorantar ƙasa, kin tsaya tare da ni cikin mutunci, haƙuri da sadaukarwa,” in ji Shugaban.
Ya ce Oluremi ta kasance abokiyar shawara da aminiya ta musamman, kuma abin koyi ga ’ya’yansu da jikokinsu, tare da kasancewa alamar tausayi da ƙarfi ga al’ummar Najeriya.
Shugaba Tinubu ya kara da cewa ƙasar nan ta amfana da sadaukarwar Uwargidan Ƙasa, wadda ta yi ayyuka masu yawa a shiru ba tare da neman yabo ba.
Ya yi addu’ar Allah ya ƙara mata lafiya da kwanciyar hankali, yana mai cewa: “Barka da zagayowar ranar haihuwa ta 65, Oluremi.
“Ina ƙaunarki fiye da da, kuma ina alfahari da kasancewa tare da ke.”acewar Sanarwar

