Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gaji asusun gwamnatin da ta gabata babu kuɗi a ciki,Inda yace abinda aka bar masa a wani daga cikin asusu bai wuce naira dubu tara ba (₦9,000) kacal.
Amma yanzu, an samu farfadowar tattalin arziki inda asusun gwamnati ke cike da biliyoyin naira
Gwamnan ya yi wannan bayani ne a yammacin ranar Alhamis yayin bikin raba takardun ɗaukar aiki (permanent da pensionable appointment) ga malaman BESDA 4,315 a Kano.
Bayanin hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Hon.Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Gwanna Yusuf ya zargi gwamnatin baya da yin sakaci da dukiyar jama’a, ciki har da ɗaukar masu ba da shawara kan haraji fiye da 128 ba tare da wani ainihin sakamako ba.
“Idan suna da hujja, su fito su nuna aikin da suka yi a Kano”in ji sanarwa.
Yace amma abin da suka yi shi ne sun ƙarar da dukiyar gwamnati har suka bar jihar cikin bashi a hannun bankuna.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ta mai da hankali wajen kyakkyawan amfani da kuɗaɗen jama’a, rufe dukkan hanyoyin zubar da su, da tabbatar da cewa dukiyar jihar tana amfani ga mutane, ba ga shugabanni ba.
“Mun sadaukar da jin daɗinmu don ganin cewa kuɗin Kano yana tafiya wajen mutane, ba wajen shugabanni ba.
“Yace wannan shi ne ka’idarmu, kuma ba za mu taɓa sassauci a kai ba,” in ji gwamna Yusuf.
Haka kuma, gwamnan ya bayyana ci gaban da aka samu a sakamakon jarabawar NECO ta shekarar 2025 a Kano a matsayin shaida ga tasirin jarin da gwamnati ta sanya a fannin ilimi.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da zuba jari a fannin ilimi, lafiya da ayyukan raya ƙasa, tare da kiyaye gaskiya da rikon amana duk da sukar da ke tasowa daga ‘yan adawa.

