Makarantar Prime College a Kano ta yi watsi da umarnin Hukumar Kula da Makarantun Masu Zaman Kansu na dakatar da ayyukanta saboda rikicin karin kuɗin makaranta, inda ta bayyana matakin a matsayin anyi ne ba bisa ƙa’ida ba.
TST Hausa ta rawaito cewa a watan Yulin shekarar 2025 ne makarantar ta sanar da karin kuɗin makaranta na zangon karatun 2025/2026, tare da hujjar cewa hauhawar farashin kayayyaki, da kula da ingancin koyarwa da kuma gyare-gyaren kayayyakin makaranta ne suka tilasta hakan.
A wata sanarwar da shugaban hukumar makarantar ta Prime Aliant Qais Conrad Laureate ya fitar ya ce kafin daukar matakin fiye da kaso 94 cikin 100 na iyaye sun amince da karin,inda mutane kalilan ne ba su amince da karin ba.
Makarantar ta kira matakin rufe ta a matsayin cin zarafi.
Acewar Sanarwar kafin rufe makarantar shugaban hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta Jihar Kano Baba Abubakar Umar, ya ziyarci makarantar tare da wasu daga cikin iyaye, inda aka kafa kwamiti na rikon kwarya na PTA mai wakilan iyaye da malamai.
Kwamiti ya kada kuri’a ya kuma amince da karin kuɗin makarantar.
Duk da haka, hukumar ta sake bayyana cewa tattaunawar ba ta kammalu ba, tare da bayar da umarni a soke karin kuɗin.
A cewar Prime College, kotun majistare ta Kano ta bayar da hukunci na dakatar da aiwatar da sabon karin kuɗin makaranta, amma ba ta bayar da umarni na rufe makarantar baki ɗaya ba, kamar yadda wani aka wallafa a jaridun kafafen sadarwa.
Makarantar ta ce ta garzaya kotu domin kare kanta, tana mai cewa hukuncin zai jefa ɗalibai cikin rasa karatu
Sanarwar ta roki gwamna Yusuf ya shiga tsakani Inda tace ko rana guda aka rufe makarantar zai kawo cikas ga Karatun yara.
TST Hausa ta rawaito cewa a baya bayan nan ne Kwamared Baba Abubakar Umar ya bada umarni ga Iyayen yara ko al’umma su kai karar duk wata makaranta da ta kara kuɗin makaranta domin daukar mataki.

