Shugaban majalisar limaman masallatan Juma’a na Jihar Kano, Sheikh Muhammad Nasir Adam, ya bukaci limaman masallatai a fadin jihar da su karkatar da hudubobin sallar Juma’a ta wannan mako kan illolin sakin harshe da kuma muhimmancin zaman lafiya a cikin al’umma.
A wani sakon murya da shugaban majalisar ya rabawa manema labarai ciki harda TST Hausa, Sheikh Adam ya bayyana cewa harshen mutum na iya zama silar tada rikici ko kuma samar da zaman lafiya.
Ya jaddada cewa wajibi ne al’ummar Kano su kasance masu yada kyawawan dabi’u da son lumana a tsakaninsu.
Sheikh Adam ya kuma gargadi jama’a da su yi hattara da kalaman su, domin gujewa fitina da rashin jituwa, yana mai cewa zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma.
A karshe, ya yi addu’a Allah ya ba jihar Kano da Najeriya baki ɗaya zaman lafiya, tare da bai wa shugabanni a matakai daban-daban ikon tafiyar da jagoranci cikin nasara.
TST Hausa ta rawaito cewa watakila kiran majalisar na gabatar da huduba akan bukatar kyautata harshe na da nasaba ne da shirya mukabalar da ta dauki hankali Kwanan nan tsakanin wasu sha’irai wato Usman mai dubun Isa da Shehi mai Tajul’izzi kan wata masalaha ta addini.

