Tsohon hadimin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje,a bangaren yada labarai Hon. Shehu Isa Direba ya bayyana goyon bayansa ga shirin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na samar da doka da za ta hana kwararowar ’yan gudun hijira cikin jihar.
A cewar tsohon hadimin, wannan mataki ya dace da bukatar tabbatar da tsaron mutanan Kano da zaman lafiyarsu inda ya ce tun da dadewa ya kamata a ɗauki irin wannan mataki,amma aka bar jaki ana dukan takki.
Ya kara da cewa kwararowar ’yan gudun hijira ba tare da tsari ba na iya jefa al’umma cikin barazana, don haka ya bukaci a hanzarta aiwatar da wannan dokar domin amfanin kowa.
Shehu Isa Direba ya ce duk wani abu da zai ciyar da al’umma gaba suna goyon bayansa a jihar Kano.
TST Hausa ta rawaito cewa gwamnatin Kano ta ce shirin samar da dokar ya biyo bayan damuwar da ake nunawa kan yadda ƙara yawan ’yan gudun hijira ke iya haifar da ƙalubale ga tsaro da tattalin arzikin jihar.
Kwamishinan addinai na Jihar Kano Sheikh Ahamad Tijjani Awwal shine ya bayyana bukatar samar da dokar hana kwararowar yan gudun hijra jihar Kano.
Ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a yammacin ranar Talata.

