Gwamnatin Jihar Kano ta fara nazarin yiwuwar samar da wata doka da za ta takaita ko ta hana kwararowar ’yan gudun hijira daga wasu sassan ƙasar nan zuwa cikin jihar barkatai ba bisa ka’ida ba.
Kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano Sheikh Ahmad Tijjani Auwal shine ya shaida hakan a ganawarsa da manema labarai a gidan Radiyon Rahma bayan kammala shirin barka da rana.
Kwamishinan yace gwamnatin Kano ta damu matuka kan yadda manyan mata da yan mata da yara kanana ke ragaita a cikin birnin Kano da kewaye wadanda kuma yawancinsu yan gudun Hijra ne daga wasu jihohin dake makotaka da Kano.
Yace babbar damuwar shine ko an mayar dasu garuruwansu na asali sai sun dawo Kano,Yana mai cewa gwamnanatin Kano ta sha killace su a basu wajen zama amma a karshe su gudu su koma bara ko ayyukan da suka saba da addinin musulunci da zamantakewar mutanan Kano.
Idan akwai doka zata bada damar bayyace matakin da za’a dauka akan irin wadannan mutane,Inji Sheikh Ahamad.
Kwamishinan na addinai sheikh Ahamad Tijjani yace a kowacce rana sai an samu ƙaruwar yawan ’yan gudun hijira zuwa cikin birnin Kano ko kewaye abinda ke ƙara haifar da ƙalubale a fannin tsaro, da inganta muhalli da kuma walwalar jama’a.
Yace gwamnati ba zata iya daukar nauyin duka yan gudun Hijra dake tururuwa zuwa Kano ba ,dan haka yace zai tura bukatar samar da doka mai tsauri ga gwamnan Kano zuwa majalisar dokokin jihar domin neman amincewarta.
Yace manufar samar da dokar ita ce kare al’ummar jihar daga matsalolin da ke biyo bayan shigowar jama’a masu yawa ba tare da wani tsari ba, da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Kano.
TST Hausa ta rawaito cewa kwamishinan ya nuna wannan damuwar ne bayan samun rahoton yadda mata da yaransu ke kwana a karkashin gadojin birnin Kano da kasuwanni da wasu ma’aikatun gwamnati wanda hakan acewarsa barazana ne ga tsaro da kuma koshin lafiyar irin wadannan mutanan.
“Muna samun labarin yadda ake amfani da halin da irin wadannan mata ke ciki ana aikata badala da su a dan haka ba zamu bari ba”In ji Kwamishinan

