Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta da wani abin da take boyewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati, domin an dauki shugabanci ne bisa gaskiya da amana.
Gwamna Yusuf ya shaida hakan ne a taron karawa Juna sa ni na kwanaki biyu da ma’aikatar yaɗa labarai karkashin jagorancin kwamishina Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ta shiryawa kungiyoyin fararen hula 250.
TST Hausa ta rawaito cewa kungiyoyin fararen hular sun samu halarta ne daga jihohi daban daban na Najeriya.
Bitar irinta ta farko mai taken:
“Ƙarfafa kungiyoyin farar hula a Kano domin samar da ci gaban ƙauyuka mai dorewa, haɓaka haɗin kai, da kuma karfafa shiga dimokuraɗiyya a matakin ƙasa ”
An shirya shi ne a dakin taro na jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu dake kofar Gadan kaya a birnin Kano.
Gwamna Yusuf wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo yace gwamnati na ganin kungiyoyin fararen hula a matsayin abokan hulɗa wajen tabbatar da ci gaban jihar, tare da bin diddigin duk wani mataki da gwamnati ke dauka domin ganin an samu gaskiya da adalci a tafiyar da mulki.
Ya yabawa ma’aikatar yaɗa labarai abisa shirya taron yana mai cewa hakan ya kara nuna cewa gwamnatin bata shakkar fito da abubuwanta fili musamman Kashe kuɗaden gudanarwa.
Mataimakin gwamnan yace gwamnatin Kano ta yan gwagwarmaya ce ,yana mai cewa kowa ga ganshi gwagwarmaya ya keyi domin kawo cigaba mai dorewa.
Kwamared Gwarzo yace irin wannan gwagwarmaya na kwatowa takala Yan cinsa shine ka tabbatar da dorewar demokaradiyya, musamman bangaren ilimin talaka da lafiyarsa da sauran bukatu.
“Gwamnatinmu a bude take tare da Jan kowa a jika,cikin gaskiya da rikon amana da kuma daidaito”Inji Gwarzo.
Tun da farko, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya shaida cewa taron zai ƙarfafa fahimtar juna tsakanin gwamnati da al’umma, musamman ta fuskar isar da sahihan bayanai da kuma ƙarfafa dimokuradiyya.
Wayya yace duk wata gwamnati da ta hada kai da kungiyoyin fararen hula to wannan gwamnatin bata shayin fito da abinda ta keyi fili kowa ya gani.
Wasu daga cikin kungiyoyi fararen hula da Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya gayyata,sun nuna gamsuwarsu da shirya musu taron.
Sun kara da cewa abinda yawancin gwamnatoci ba su fahimta ba shine sun dauka kungiyoyin fararen hula suna zama ne a matsayin fito na fito da gwamnati shiyasa basa jansu a jika.
Kwamared Salisu Ditol wanda na daya daga cikin mahalarta taron yace ya zama wajibi su jinjinawa gwamnanatin Kano saboda fahimtar juna da aka samu tsakaninta da kungiyoyin fararen hula.
Ditol yace amma hakan ba yana nufin idan sunga wani abin gyara ko shawara su gaza baiwa gwamnatin ba.

