Gwamnatin Jihar Kano ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da karin kuɗin makaranta ba bisa ƙa’ida daga wasu makarantu masu zaman kansu ba, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubalen tattalin arziki.
Gwamnatin ta bada wa’adin mako biyu a kai mata rahoton duk wata makaranta mai zaman kanta da ta kara kuɗin makaranta aga matakin da za’a dauka akanta.
Shugaban hukumar kula da makarantun masu zaman kansu da na sa kai ta Jihar Kano Kwamared Baba Umar ne ya sanar da haka a cikin shirin gwamnati da jama’a da aka gabatar tare da shi a gidan Radiyon Rahma a Kano a karshen mako.
Ya ce gwamnati ta samu korafe-korafe daga iyaye kan yadda ake ƙara kuɗin makaranta ba tare da tuntubar su ko kuma neman izinin gwamnati ba.
Yace ga duk mai korafi akan makarantar yayansa ya garzaya zuwa ofishin wucin gadi na hukumar dake gidan Malamai bayan tsohon dogon banki.
Ko a kira wannan lambar wayar 09033300034 ko kuma tura sakon karta kwana.
Baba Umar ya bayyana cewa an kafa wani kwamitin musamman domin bincikar dukkan makarantun da suka ƙara kuɗi, tare da gano irin karin da ake yi da kuma dalilan da shugabannin makarantun ke bayarwa.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta yi tattaunawa kai tsaye da ƙungiyar makarantun masu zaman kansu domin samar da mafita mai dorewa, wacce za ta kare muradun ɗalibai da iyaye ba tare da tauye hakkokin masu zuba jari a fannin ilimi ba.
Haka kuma, gwamnati ta yi gargadi cewa idan aka tabbatar da yin karin kuɗin makaranta ba bisa ƙa’ida ba, za ta ɗauki matakan doka,ciki harda kai makarantar kotu da kuma dakatar da izinin gudanar da makarantar ko kuma ɗaukar wasu matakan ladabtarwa da suka dace.
TST Hausa ta rawaito cewa shugaban ya kuma shawarci iyaye da su rika kai rahoton kowace makaranta da ta ƙara kuɗin makaranta ba tare da izini ba, domin hakan zai taimaka wajen samun sahihan bayanai da kuma bin diddigin lamarin.
A cewarsa, manufar gwamnatin Kano ita ce ta tabbatar da cewa kowa ya samu damar karatu cikin sauƙi, ba tare da ƙarin nauyin da zai jawo barin makaranta ba.

