Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi samame a ranar Takutaha a sassa daban-daban na birnin Kano, inda ta kama wasu matasa da dama bisa tuhumar sanya kaya da suka saba da koyarwar addinin Musulunci da kuma al’adun Hausawa.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an Hisbah sun shiga cikin taron masu zagayen na Takutaha a tituna da wuraren biki da matasa ke taruwa, inda suka gano wasu daga cikinsu cikin tufafi da aka bayyana a matsayin “marasa kamun kai” da kuma “marasa dacewa” da darajar al’umma.
Mataimakin kwamandan Hisba a bangaren ayyuka na musamman Dr Mujahedeen Aminuddeñ Abubakar shi ne ya tabbatar da faruwar kama matasan, yana mai cewa wannan matakin ya yi daidai da tsarin hukumar na tsare tarbiyya, da kuma tabbatar da bin ka’idojin addini musamman a lokutan bukukuwan da kan tara matasa da dama.
Ya kara da cewa hukumar ba za ta lamunci shigar da zai lalata tarbiyyar matasa ba, kuma za ta ci gaba da gudanar da irin wadannan sintiri domin kare al’umma daga dabi’un da ba su dace ba.
Sai dai wasu daga cikin mazauna birnin sun nuna goyon baya ga wannan mataki, suna mai cewa ya dace a rika kula da irin tufafin da ake sawa a bainar jama’a, yayin da wasu kuma suka bukaci hukumar ta yi amfani da hanyoyin wayar da kai maimakon kama mutane kawai.
Daga cikin wadanda aka kama harda matasan da suka bade kansu da toka.
TST Hausa ta rawaito cewa a halin yanzu, wadanda aka kama suna tsare a ofishin hukumar, inda ake ci gaba da bincike kan lamarin kafin daukar matakin da ya dace a kansu.
Hisba ta yaba da yadda aka gudanar da bikin Takutaha din ba tare da fadan Daba ko kwacen waya ba.

