Matatar man fetur ta Dangote ta musanta zargin da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Najeriya (NUPENG) ta yi mata na tauye haƙƙin ma’aikata da yunƙurin mamaye kasuwa.
A cikin wata sanarwa,Matatar ta ce ba gaskiya ba ne cewa ta hana ma’aikata shiga ƙungiyar kwadago ko tilasta direbobi yin watsi da ‘yancinsu.
Dangote ya kuma bayyana cewa shirin fitar da motocin jigilar kaya masu amfani da iskar gas CNG ba domin rusa ayyuka ba ne, illa ma don samar da ƙarin guraben aiki.
Ya ce kowace mota za ta ɗauki ma’aikata shida, tare da albashi da ya fi mafi ƙarancin ƙasa, da tallafin lafiya, da fansho da gidaje.
Kamfanin ya bayyana cewa yana shirin fitar da motoci 10,000 kafin ƙarshen wannan shekara, abin da zai iya samar da fiye da ayyuka 60,000 kai tsaye.
Dangote ya kuma karyata zargin cewa yana shirin ƙara farashin man fetur, inda ya ce a maimakon haka, farashin dizal ya ragu da sama da kashi 30 cikin 100 a shekara guda, yayin da farashin fetur a Najeriya ya fi na wasu ƙasashen duniya araha.
Kamfanin ya ƙara da cewa ya riga ya zuba jari sama da Naira biliyan 720 a harkar CNG, tare da samar da dubban ayyuka da kuma tallafa wa gina ababen more rayuwa a ƙasar.

