Kungiyar Twins Empowerment Initiative Kano ta bayyana godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa tallafin da ya bayar wajen tabbatar da cewa tagwayen da aka raba a ƙasar Saudiyya za su ci gaba da samun kulawa ta musamman tare da ɗaukar nauyin karatunsu har zuwa matakin jami’a.
Shugaban ƙungiyar, Malam Hassan Magashi, tare da Sakataren ƙungiyar, Malam Hassan Kabara, sun bayyana farin cikinsu bisa wannan mataki da gwamnatin Kano ta ɗauka, wanda ya nuna jajircewar ta wajen tallafawa yara, musamman tagwaye, da kuma kare martabar su.
Kungiyar ta kuma mika godiya ga Gidauniyar Sarki Salman bin Abdul’aziz Al Saud da kuma Ofishin Jakadancin Saudiyya a Najeriya, bisa ɗaukar nauyin aikin raba tagwayen da kuma kulawa da aka yi musu tsawon shekaru biyu a ƙasar mai tsarki.
A cewar ƙungiyar, wannan aiki ya zama tarihi mai ɗauke da darasi da kuma alheri ga iyayen tagwayen, al’ummar Kano, da Najeriya baki ɗaya.
Twins Empowerment Initiative Kano ta kuma sha alwashin ci gaba da mara baya irin waɗannan shirye-shirye da kuma kare muradun tagwaye a cikin al’umma.
Kungiyar ta yi addu’ar Allah ya saka da alheri ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, ga gwamnatin Saudiyya, da duk masu ruwa da tsaki da suka ba da gudunmawa wajen tabbatar da wannan aiki cikin nasara.

