Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da gobe Juma’a, 19 ga Rabi’ul Awwal, 1447H, wanda ya yi daidai da 12 ga Satumba, 2025, a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwan ranar sunan haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai na Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya, ya sanyawa hannu a madadin gwamnatin Kano.
Sanarwar ta bayyana cewa hutun zai bai wa jama’a damar gudanar da bukin Takutaha, wato bikin cika kwanaki bakwai da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW)
Gwamnatin ta kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin tunani da kuma koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW), tare da roƙon Allah ya ba da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
TST Hausa ta rawaito cewa gwamnati na taya al’ummar Musulmi murnar wannan gagarumin biki na Mauludi, tana fatan ya zo da alheri ga kowa da kowa.

