Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta yi karin haske kan zargin da wasu daga cikin tsaffin hadiman tsohon gwamnan jihar Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje ke yi wa Shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Sale Pakistan cewa ya gaza gabatar da rahoton aikin Hajji na shekarar 2025 kamar yadda doka ta tana da.
A wata tattaunawa ta wayar salula da daraktan yaɗa labarai ta hukumar aikin Hajji ta Najeriya Hajiya Fatima Sanda Usara ta yi da TST Hausa,tace a bisa doka hukumar ta aikin Hajji tana gabatar da rahoton ta ne bayan watanni uku da kammala aikin Hajji a duk shekara.
Ta nemi yan siyasa da su daina kokarin tsoma hukumar ta aikin Hajji a cikin harkokin siyasa.
Sanda Usara tace korafe-ƙorafe da wasu mutane suka kai hukumar EFCC kan zargin bacewar wasu kuɗade na daga cikin abinda ya janyo tsaiko wajen gaza gabatar da rahoton aikin Hajji na 2025 akan lokaci.
Saidai tsohon hadimin tsohon gwamnan jihar Kano Dr Ganduje wato Hon Shehu Isa Direba wanda yana daga cikin masu neman dalidan da suka janyo aka samu tsaiko wajen gabatar da rahoton akan lokaci yace hakan ya sake basu kwarin guiwa na cigaba da zargin rashawa a cikin aikin Hajjin na 2025.
Amma a martanin da ta mayar daraktan yaɗa labarai ta hukumar NAHCON Hajiya Fatima Sanda tace babu abinda hukumar keyi a boyewa yan Najeriya kuma zata sanar da jama’a sakamakon rahoton na aikin Hajjin da ya gabata nan da dan lokaci kadan.
Game da zarge -zargen cin hanci da rashawa da ake tuhumar dan Uwan Farfesa Pakistan na kuɗi miliyan dubu 50, NAHCON tace wasu mutane ne suka gabata da korafi zuwa ga hukumar EFCC kuma ta fara bincike dan haka tace har yanzu akan zargi ake,kuma ba kowanne zargi ne ke zama tabbas ba.
“Duka wadannan zargen zargen da kuma tuhume tuhume da jama’a su ke yiwa Shugaban hukumar ta NAHCON Farfesa Abdullahi Sale Pakistan hakan bai hana shi yin aikinsa da ya saba ba”,in ji Fatima
Daga nan ta nemi jama’ar Najeriya suyi watsi da duk wani abu da yaci karo da abinda doka tace game da aiki hajji da hukumar ke tsarawa a duk shekara.
NAHCON ta kuma gargadi masu yada zarge-zargen marasa tushe da su daina amfani da aikin Hajji a matsayin abin siyasa, tana mai jaddada cewa aikin ibada ne da bai kamata a gurɓata shi da siyasa ba.
Idan za’a iya tunawa,a baya bayan nan Shehu Isa Direba Shehu Isa ya yi zargin cewa Farfesa Abdullahi Sale Pakistan ya kunyata Sanata Barau Jibiril da dukkanin wadanda suka bada gudun mowa wajen tantance shi a majalisar dattawa kafin bashi wannan matsayin na shugaban NAHCON.

