Lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana (SAN), ya yi Allah-wadai da hukuncin daurin shekaru uku da aka yanke wa wani mai gyaran mota mai shekaru 28 da haihuwa, Akeem Jimoh, da aka same shi da laifin satar doya a jihar Osun.
An yankewa Akeem hukuncin ne a kotun Majistire dake Osogbo, bayan ya amsa laifin satar doya mai darajar kudi naira 35,000 da ake zarginsa da shi.
A yayin da aka tambaye shi dalilin aikata laifin, Akeem ya shaida wa kotu cewa yunwa ce ta sanya shi satar doya guda 17, inda ya roki kotu ta tausaya masa.
Sai dai mai shari’a, Muibah Olatunji, ya yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari tare da aiki mai wahala, ba tare da wani zabin biyan tara ba.
Da yake tsokaci a kan hukuncin a wata sanarwa da ya fitar, Falana ya bayyana cewa akwai bukatar a sake duba tsarin yanke hukunci a Najeriya domin ya zama daidai da zamantakewa da adalci.
Ya kuma tambayi dalilin da zai sa a ci gaba da bata kudaden jama’a wajen kula da wadanda aka daure saboda kananan laifuka irin na Akeem.

