Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Rano,da Kibiya da Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya yi kira ga al’ummar mazabarsa da su yi rijistar mallakar katin zabe na dindindin, wato PVC.
Rirum ya nemi duk wanda bashi da katin zaben ya je ofisoshin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC a yankunansu domin mallakar katin.
Rurum ya ce waɗanda ba su da katin zabe, da kuma wadanda ke da matsaloli da katin nasu, ko kuma suke bukatar sauya rumfar kada kuri’a, su yi amfani da wannan dama domin gyara matsalolinsu kafin lokaci ya kure musu.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai,Hon. Fatihu Yusuf Abdullahi, ya fitar, Rurum ya kuma shawarci iyaye da masu ruwa da tsaki da su tura ‘ya’yansu da suka kai shekarun yin zabe domin su yi rijista.
Hon. Rurum ya jaddada cewa yin zabe na cikin haƙƙin ɗan ƙasa da kuma muhimmin ginshikin dimokuraɗiyya, inda ya ce: “Kowane ɗan ƙasa na da hakkin ya kada kuri’a, sannan kuma ya kare kuri’arsa, domin hakan shi ne ainihin dimokuraɗiyya.

