Mai martaba sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi na II ya kammala Karatun digiri na Uku a London.
An gudanar da bikin kammala Karatun ne a Friends House,dake birnin London, a ranar Alhamis.
Bikin ya fara da liyafa ta musamman da Mataimakiyar Shugabar Jami’ar School of Oriental and African Studies (SOAS) ta shirya, inda gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da takwaransa na Abia, Alex Otti, suka halarta.
Sarki Sanusi ya gabatar da takardar bincikensa mai taken:“Codification of Islamic Family Law as an Instrument of Social Reform: A Case Study of the Emirate of Kano and Comparison with the Kingdom of Morocco.”
Wato nazarin yadda tsara dokokin shari’ar Musulunci na iyali zai iya zama hanyar gyaran zamantakewa, musamman a Kano, tare da kwatanta tsarin da na Morocco.
Kwamitin masu tantance binciken ya bayyana cewa aikin da sarki Sanusi ya yi yakai matsayi na musamman, inda ba a ga buƙatar wani gyara ba, kana ɗaya daga cikin malamai ya bayyana shi da cewa komai ya kammala yadda ake so.
Sarki Sanusi ya fara wannan karatu ne bayan sauke shi daga sarautar Kano a shekarar 2020, inda ya koma Birtaniya ya mai da hankali kan bincike.
Kafin haka, ya samu digirin girmamawa a fannin kudi daga wannan jami’ar ta birnin London a 2019, tare da zama mai bincike a jami’ar Oxford.
TST Hausa ta rawaito cewa tarihin karatunsa ya nuna cewa ya yi digiri na farko a fannin tattalin arziki a 1981, ya sake samun digiri na biyu a bangaren tattalin arziki, sannan ya sake yin wani digiri na biyu a addinin Musulunci da fiƙihu a 1997.

