Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya zargi jam’iyyun adawa da kokarin tunzura gwamnatinsa da jam’iyyar APC su fara yaƙin neman zaɓen 2027 tun lokacin baiyi ba.
Sai dai Tinubu ya ce ba zai bari hakan ya karkatar da hankalinsa daga shugabantar Najeriya ba.
Yayin da yake ganawa da gwamnonin Arewa maso Gabas a fadarsa dake Abuja, Shugaba Tinubu ya yaba da ƙoƙrinsu wajen yaƙi da rashin tsaro tare da alƙawarin yin aiki da su kan batun samar da ’yan sandan jihohi da kuma ayyukan gina hanyoyi.
TST Hausa ta rawaito cewa a yayin ganawar gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, wanda ya yi magana a madadin sauran gwamnonin, ya tabbatar wa shugaban ƙasa da goyon bayansu.
Ya bayyana matsalolin tsaro a Arewa maso Gabas tare da roƙon ƙarin tallafin Gwamnatin Tarayya.
Gwamnonin sun kuma roƙi shugaban ƙasa ya kammala manyan hanyoyi, ya ci gaba da aikin haƙo mai a Kolmani da Tafkin Chadi, da kuma ci gaba da ayyukan soji a yankin.

