Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta gurfanar da wani magidanci mai suna Ahmad Usman a gaban Kotun Shari’ar Musulunci dake unguwar Danbare,a karamar hukumar Kumbotso bisa zargin hada kai da ‘yan daba tare da aikata tashin hankali a unguwar Dabai dake karamar hukumar Dala.
An gurfanar da Ahmad ne a gaban mai shari’a Alƙali Munzali Idris Gwadabe, bayan wani magidanci mai suna Abba Sha’aibu Isa tare da wasu mutane goma da suka shigar da ƙara a kansa, suna zarginsa da kai musu hari da taimakon wasu matasa ‘yan Daba.
A cewar masu ƙara, lamarin ya faru ne a lokacin da suke zaune a kofar gida, inda Ahmad ya yaje wajen da wasu yan Daba Inda yake fada musu bakaken magana cewa wani a cikinsu ya sayo makara da aka kaita cikin masallacin unguwar ta Dabai.
TST Hausa ta rawaito cewa Ahmad yayi korafin wannan makara da aka ajiye a masallacin tana firgita yayansa wani lokacin har dashi kansa idan sun shiga zasuyi Sallah.
A zaman kotun, lauyan gwamnatin Jihar Kano, Barista Musbahu Usman, ya nemi a ba da lokaci domin jiran shawarar Ma’aikatar Shari’a ta jihar Kano kan wannan sarkakiya.
Alƙali ya daga zaman shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Oktoba, 2025.
Bayan zaman kotu, wakilin TST Hausa Nazifi Bala ya tuntubi masu ƙara inda suka nemi ayi musu adalci saboda tsorata su da akayi da yan Daba.
Amma kuma wanda ake tuhuma, ya ki cewa komai.

